Pair of Vintage Old School Fru
Sulaiman20Ibn20Hujjah 2
Barka20Da20Zuwa
Shafi20Mai20Albarka



¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶¶

Zaka iya kiran wayata tanan
HomeBlogAbout MeBayani Akan AZUMIAikin Hajji da UmaraMa anar Shi aAbin da Aka HanaSamun FalalaKasuwanci Mai RibaMahimmancin Addu o iBayanin ZakkaSALLAMATA A MUSULUNCITSARKITAUHEEDI DA AQIDAAYYUKAN ZUCIYAMAHIMMANCIN DA AWATAMBAYA DA AMSASheikh jafar mahmud AdamWadansu websides


SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTTUKAN MALUMAN SUNNAH


Sheik Lawan Abubakar Gadon Kaya tafseer2017



02/05/24
FB Pantami


Ibn20Hujjah
Source: Google news
0Mozilla/5.0




SULAIMAN Ibn Hujjah

* No categories

Online: Guests: 1


Sulaiman20 FaceBook


BAYANIN ZAKKA

Zakka tana wajaba abangarori guda hudu.
*NADAYA: Dabbobin gida ( Rakumi, Sa, da Akuya/tinkiya) Wadanda Ake Musu lakabi da sa'ima (wato; masu kiwatan mafi rinjayen shekara daga ciyawar jeji; SHI WANNAN SHARADIN AKWAI SABANIN MALUMA AKANSA).
*NABIYU: Abubuwan da suke fitowa daga kasa.
NA UKU: Dukiya.
*NAHUDU: Cikar mallaka.
*NABIYAR: Cikar shekara -wato shekara cikakkiya; in ban da abubuwan da suke fita daga kasa.

**ZAKKAR DABBOBIN GIDA**
Wannan nau,i uku ne
(1) Rakuma
(2) Shanu
(3) Tumaki
Kuma zakka ya zama wajibi a cikinsu akwai sharuda guda biyu:
(1) Suyi kiwo (cikin ciyawar da allah ya tsirar) gwargwadon sheka ko kusa da haka.
(2) Yazama an tanade sune don tatsa da yaduwa , ba don aiki ba. amma idan sun kasance an tanade sune domin kasuwanci ta ana yi masu zakkan kayan kasuwa ne.

**ZAKKAR RAKUMA ITACE**
Daga rakumi daya zuwa hudu babu zakka akansu.
Daga biyar zuwa tara za a fitar musu da akuya daya.
Daga goma zuwa sha hudu za a fitar musu da akuyoyi biyu.
Daga goma shabiyar zuwa goma sha tara za a fitar musu da akuyoyi uku.
Daga ashirin zuwa ashirin da hudu za a fitar musu da akuyoyi hudu.
Daga ashirin da biyar zuwa talatin da biyar za a fitar da bintu makhad.( rakuma wacce ta cika shekara).
Daga talatin da shida zuwa arba'in da biyar za a fitar musu da bintu labun( rakuma mai shekara biyu).
Daga arba'in da shida zuwa sittin za a fitar musu da hikka( mai shekara uku).
Daga sittin da daya zuwa saba'in da biyar za a fitar musu da jaz'a( mai shekara hudu).
Daga saba'in da shida zuwa casa'in za a fitar musu da bintu labun guda biyu.
Daga casa'in da daya zuwa dari da ashirin za a fitar musu da hikka guda biyu.
Idan an sami kari akan dari da ashirin sai a fitar wa kowane hamsin( hikka) kowane Arba'in kuma ( bintu labun).

**ZAKKAR SHANU**
Daga daya zuwa ashirin da tara babu zakka akansu.
Daga talatin zuwa talatin da tara za a fitar musu da tabi'un namiji ko mace( sune 'yan shekara guda).
Daga arba'in zuwa hamsin da tara za a fitar musu da Musinna namiji ko mace( sune 'yan shekara biyu).
Idan suka kai guda sittin sai a fitar da ( tabi'un) ga kowane talatin.
kowane arba'in kuma ( musinna).
**ZAKKAR AWAKI**
Daga daya zuwa talatin da tara babu zakka akansu.
Daga arba'in zuwa dari da ashirin za a fitar musu da akuya guda daya.
Daga dari biyu da daya zuwa dari uku da casa'in da tara za a bada akwaki uku.
Idan adadinsu suka kai dari hudu ko fiye da haka to kowane dari za a bayar da akuya daya.
Azakkan awaki ba a daukan bunsuru garke, haka kuma ba a karbar mai harari garke, ko wadda take shayar da danta, ko mai ciki, ko wacce take jagorantar sauran garken.

**ZAKKAR ABUBUWAN DA SUKE FITOWA DAGA KASA**
Zakka tana wajaba atsirrai daga kwayoyi da "ya 'yan itatuwa da sharudda uku.
(1) Zamowar tsirran daga abin da ake awo ko tanadi ne, kamar sha'ir ko alkama, daga cikin kwayoyi, da kuma kamar inabi da dabino daga cikin 'ya 'yan itace.
Amma abin da baza a iya awonsa ko tanadinsa ba kamar kwarran abubuwa (ganye,tumatu d,s) da kuma abubuwan da suke bunkudo kasa(kamar su gwaza, da doya,dankali, d,s) da abubuwan da suka yi kama da su, to babu zakka acikinsu.
(2) CIKAR NISABI: Shi ne ya kai kilo giram 653 ko fiye.

(3) Kuma tsirran su zamo mallakarsa ne a lokacin da zakkar ta wajaba, kuma lokacin wajibcin: Shine fara nunar 'ya yan itatuwa (kamar dabino in aka samu daidaiku daga cikinsu sun fara ja-ja-ja-ja), shi kuma fara nunar kayan marmari shine idan ya yi ja ko fatsi-fatsi.
Yayin da shuka kuma (kwaya) bayyanan nagartarsa shine ya yi karfi (lokacin nuna), ya kuma bushe.
Yana wajaba a fitar da ( 10%) kashi goma cikin dari a cikin abin da akayi bayinsa ba tare da wahala ba.

Kamar wanda aka yi ban ruwa da ruwan sama ko na rafuka. Za a kuma fitar da ( 5%) Kashi biyar cikin dari a cikin abinda aka yi ban ruwa da wahala ko daukar nauyi kamar ruwan da ake fitar da shi daga dam ko masu kama da shi.

Amma abin da aka yi masa bayi da wahala a wassu kwanakin shekara, wassu bangarorin kuma ba tare da wahala ba, ta za a kimanta shi da mafi yawa daga cikinsa, wahalar ne ko kuma rashinta.

**ZAKKAR DUKIYA**
Dukiya kashi biyu ce:
(1) Zinari: kuma babu zakka a ciki har sai yakai (giram 85).
(2) Azurfa: kuma babu zakka a ciki har sai sunkai (giram 595).
Kuma babu zakka a cikin sulalla ko kudin takardu har sai kimar zakkar dukiya itace: daya bisa arba'in (biyu da rabi bisa dari 2 .5%).
Kayayyakin adon da aka tanade su domin amfani, babu zakka a cikinsu.
Wanda kuma akayi tattalinsa don bada hayansa (kasuwanci)ko taskancewa za a yi musu zakka.

Wanda kuma yake da dukiyar da take raguwa ta ke karuwa, sa'annan ya wahala wajen sa wa kowa ne yanki na dukiyarsa lokacin fitar masa da zakkarsa a cikinsa, to ya halatta ya kebance wani yini a shekara don ya rika fitar da zakkarsa a cikinsa.
A wannan ranar zai duba nawa ne ya mallaka, don ya rika fitar da biyu da rabin dukuyarsa cikin dari (2 1/2)% Daga cikinsu, (wato daya cikin arba'in din dukiyarsa kenan) zai yi haka koda kuwa wani bangare daga cikin kudirsa bai cika shekara ba.
Wanda kuma yake da albashi ko abin haya kamar gida ko wata kasa (gona ko waninta), idan ba a taskance wani abu daga gare shi ba, to babu zakka a cikinsa, komai yawansa.
Amma idan kuwa ya taskance wani abu daga cikinsa to sai ya fitar da zakka daga abinda ya taskacen idan ya shekara.
Idan kuma yin hakan ya yi wahala sai ya sanya wata rana daga cikin shekara domin fitar da zakkar kamar yadda ya gabata.

SHIGA NAN DOMIN SAMUN KARATUTUKAN MALUMAN SUNNAH A SAUKAKE
**ZAKKAR BASHI**
Wanda ke da bashi akan mawadaci ko ya ke da dukiyan da zai iya karbanta a ko yaushe, to ya wajaba ya bada zakkarsa - idan ya karbe shi - na abin da ya gabata daga shekaru komai yawansu.
Idan kuma karbarsa ya wahalar kamar bashin da ke kan talaka to idan ya karbe su babu zakka a cikinsu saboda ba shi da ikon jujjuya shi ( da karbarsa duk lokacin da ya so).
**ZAKKAR KAYAN KASUWA**
Babu zakka a cikinsu sai sun cika sharudda guda hudu:
(1) Ya mallaki kayan.
(2) Sa'annan ya yi niyyar kasuwanci dasu.
(3) Sa'annan kimarsu ya kai nisabi: wadda shine mafi karancin nisabin dhinari ko azurfa.
(4)Sa'annan ya cika shekara.

**ZAKKAR KONO (FIDDA KAI)**
Wannan zakkar wajibi ce akan ko wane musulmi wanda ya mallaki wata dukiya da ta karu akan abin da ya ke bukuta da iyalinsa na daren idi da ranarsa. Kimar abin da za'a bayar ga kowani mutum guda namiji ko mace shi ne: (21 /4)Kilo biyu da kwata na daga irin abincin gari.
Kuma wanda ta hau kansa dole ne yafitar da ita akan kansa da kuma duk wanda ciyarwarsa ta hau kansa; a daren idi, mustahabbi ne ya fitar da shi ranar idi kafin ayi salla matukar ya mallake shi.
Kuma baya halatta a jinkirta daga sallar idi.
Kuma yana halarta a ba mutum daya na wasu jama'a, kamar yadda za a iya ba mutane da yawa abin da ya lazimci mutum guda.

**FITAR DA ZAKKA**
Ya wajaba a fitar da zakka da gaggawa. kuma dole ne waliyyin yaro da mahaukaci ya fitar da ita daga dukiyarsu.
Kuma sunna ne a bayar da ita a bayyane.
Haka kuma mai ita ya raba ta ga wadanda suka cancance ta shida kansa (shi ma wannan sunna ne).
Kuma an shardanda wa mukallafi (baligi mai hankali) a locakin fitar da ita .
Kuma bata isa idan dazai yi niyyar budeddiyar sadaka ko da kuwa ya sadaukantar da dukiyarsa gaba daya.
Kuma yafi kyau ya sanya zakkar dukiyarsa ga fakitan garinsu,
Kuma ya halatta a dauka zuwa wani garin daban domin wata maslaha.
Kuma ta na isa kuma ta inganta a gahauta zakkar shekaru biyu idan sun cika nisabi.

**WADANDA AKE BA ZAKKA**
Su takwas ne:
(1) Fakiri
(2) Miskinai
(3) Masu Aiki A Kan Ta (ma'aikatan Zakka)
(4) Wadanda Ake Tarairayar Zuciyarsu (domin su shiga musulunci ko akara tabbata acikinsa)
(5) Masu neman 'yanci
(6) Masu bashin da yafi karfin su
(7) Masu aiki fisabilillahi
(8) Matafiyi da guzuri ya yanke masa.
ko wanne daga cikinsu ana bashi zakka.

ALHAMDU LILLAH WANNAN SHINE BAYANI AKAN ZAKKA

Ganduje Ya Tallafawa ‘Yan Gudun Hijira Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abdullahi Umar Ganduje...
MozillaOur contacts

Sulaiman20Ibn20Hujjah-1 3